On Air Now

ZANGON SAFIYAR LAHADI

5:00am - Noon

Shugaban Jami'ar Jos Ya Roki Malaman ASUU Su Dubi Allah Kuma Su Tausayawa 'Dalibai Su Komawa Bakin Aiki

Shugaban Jami’ar Jos, Farfesa Tanko Ishaya, ya yi kira ga kungiyar ASUU ta jami’ar da ta tausaya wa dalibai tare da ci gaba da harkokin koyo da koyarwa.

Ishaya ya yi kiran ne a zantawa da  manema labarai a  birnin Jos, yana mai cewa akwai bukatar malamai su koma aji  domin hana karatun jami’a durkushewa  bakai  daya.

Ya roki kungiyar da ta yi la’akari da halin da dalibai da iyaye suke ciki tare da maida takobin su cikin kube domin ci gaban ilimi a kasar nan.

Farfesa Tanko ya sake rokon mambobin na ASUU su dubi  Allah su tausayawa dalibai da iyaye su koma cigaba da koyarwa.