On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Shugaban Jam'iyyar PDP Na Kasa Yayi Baluguro Zuwa Ketare, A yayin Da Ya Mika Ragamar Jam'iyyar Ga Mataimakinsa

SANATA AYU SHUGABAN JAM'IYYAR PDP

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Dr. Iyorchia Ayu ya mika ragamar tafiyar da jam’iyyar ga matimakinsa na shiyyar Arewa Umar Iliya Damagun.

Mashawarcinsa ta bangaren yada labarai da sadarwa, Simon Imobo Tswam ne  ya baiyana haka da maraicen  ranar Talata, inda  ya baiyana cewa shugaban jam’iyyar zai yi balaguro zuwa ketare har zuwa  karshen watan da muke ciki.

Babu dai wasu dalilai da aka baiyana kan  balaguron da shugaban jam’iyyar zai yi zuwa ketare, duk da  rikicin cikin  gida da jam’iyyar  ke fama dashi, Ana saran  jam’iyyar ta  PDP  zata kaddamar da yakin neman zabenta a ranar  28 ga watan satumbar da muke ciki.

Shugaban jam'iyyar PDP da Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas

Hakan na nufin cewa  Sanata Iyorchia Ayu zai kasance baya gida Najeriya a lokacin da jam’iyyar zata kaddamar da kwamitin yakin neman zabenta na kasa  gabanin babban zaben shekara mai zuwa.