On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Shugaban Kasa Bola Tinubu Zai Gabatar Da Kasafin Kudin Shekara Mai Zuwa A Gobe Laraba

TINUBU

A jiya ne taron majalisar zartarwa na kasa ya amince da kudurin kasafin kudin shekara mai zuwa na kimanin naira tiriliyan 27 da bilyan 5, wanda hakan ya nuna an samu karin sama da Tiriliyan 1 daga ainihin naira Tiriliyan 26 da digo 1, da aka yi tsammanin za’a dora kasafin kudin mai zuwa.

Ministan kasafi da kuma tsare-tsaren tattalin arzikin kasa, Abubakar Bagudu ne  ya   sanar da amincewar ga manema Labarai na fadar  shugaban kasa, jim kadan bayan kammala zaman da aka yi.

Ya ce gwamnatin tarayya  na hasashen samun naira tiriliyan 18 daga bangaren biyan haraji a kakar kudi ta shekara mai zuwa, Inda  ya yi alkawarin yin cikakken jawabi akan kudirin kasafin kudin, da zarar shugaban kasa ya gabatar da shi a gaban hadakar zaurikan majalisun dokokin kasa.

 

A  nan kuma matukar ba wani sauyi  aka samu ba,  Ana saran  shugaban kasa  Bola Tinubu, zai gabatar da  kudirin kasafin kudin shekara mai zuwa a gaban hadakar zaurikan majalisun kasa a gobe Laraba.

Wannan ne karon farko da shugaban kasar zai  gabatar da kasafin kudi  na kimanin sama da naira tiriliyan 27 a gaban ‘yan majalisun dokokin kasa tare da yi  masu jawabi.

An samar da matakan tsaro  gabanin gabatar da kasafin kudin da za’a yi.

A wani  bangaren kuma, Shugaban Kasa  Bola  Tinubu ya sake nada  Malam Mele Kyari a matsayin shugaban Kanfanin mai  na kasa , Kamar  yadda yake kunshe cikin wata sanarwa da kakakinsa Ajuri Ngelale  ya fitar a jiya.