On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Shugaban Kasa Buhari Yace Zango Biyu Zai yi Akan Mulkin Najeriya

BORIS vs BUHARI

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da Firiyiministan Burtaniya Boris Johnson, Inda ya jaddada masa cewar zai yi zango biyu ne kacal akan mulkin kasar nan, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya kaiyade.

A wata samarwa da Kakakin shugaban kasar Femi Adesina ya fitar a Abuja, yace anyi ganawarne kan abubuwan da suka shafi taron kungiyar Kasashen Renon Ingila karo na 26 wanda  yake gudana a Kigali babban birnin kasar Ruwanda.

Kakakin shugaban kasar wanda ya baiyana cewa, Firiyiministan bashi da cikakkiyar masaniyar  tsarin wa’adin mulkin kasar nan ya ta’allaka ne a iya zango biyu, Ya  Tambayi Shugaban kasar akan ko zai kara komawa kan mulki, Kuma nan take shugaban Kasa Buhari ya baiyana cewa, Mutumin da ya fara kwatanta haka bai kai gaci ba.

Firiyiministan ya baiyana alakar dake tsakanin kasashen biyu a matsayin wata muhimmiya wadda  ta jima, sannan kuma ya mika sakon ta’aziyyarsa ga gwamnatin kasar nan akan wasu hare-hare na kwanan nan da aka kai musamman kan majami’u.

 

 

More from Labarai