On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Shugaban Kasa Buhari Zaije Kasar Ghana A Yau Talata

BUHARI

A yaune Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai halarci taron kolin shugabannin kasashen Tekun Guinea a birnin Accra na kasar Ghana.

Hadimin shugaban kasar  ta fuskar yada labarai,Femi Adesina ne ya tabbatar da  haka a Abuja,  Y ace  shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo ne zai jagoranci taron.

Ya kara da cewar  shugaban kasar  na daga cikin manyan masu gabatar da jawabi a wajen taron,wanda za’a tattauna  kan dabarun inganta tsaro da samar da zaman lafiya  da kuma yaki  da ‘yan fashin teku.