On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Bukaci Yan Najeriya Su Rika Nuna Kwarin Gwiwarsu Akan Dakarun Soji Kasar Nan.

SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su Kasance masu yakini da karfin da sojojin kasar nan ke da shi wajen kare Najeriya da kuma samar da dawwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.

A cikin wata sanarwa da Hadimin shugaban kasa ta bangaren yada Labarai  Femi Adesina, ya fitar, shugaban kasar ya baiyana haka ne, yayin da yake bude gasar sojojin ruwa ta kasa  karo na 12  ta shekarar  bana a Legas  a ranar Alhamis, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa sojojin za su ci gaba da gudanar da aikinsu na  domin  dakile  matsalolin rashin  tsaro da sauran  kalubale da kasar nan ke fuskanta.

SHUGABAN KASA BUHARI

Shi ma da yake nasa jawabin, Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya bayyana rundunar sojojin ruwan  kasar nan a  matsayin wata abokiyar  huldar ‘yan sandan jihar Legas  wajen  tsaron rayuka da kuma kare dukiyoyi.

Kazalika shima  babban  Hafsan  sojin ruwa na Kasa, Vice Admiral Awwal Gambo, Ya yi alkawarin cewa rundunar sojin ruwa za ta ci gaba da yaki da satar danyen mai da sauran laifukan fashin teku  tare da tabbatar da cewa kasar nan  ta  fice daga jerin kasashen da ke fama da matsalar fashin teku.