On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Gana Da Zababben Gwamnan Ekiti

A yaune shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Zababben Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Abayomi Oyebanji, a fadarsa dake Abuja.

Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Sanata  Abdullahi  Adamu da Gwamna  Kayode  Fayemi  sai kuma Atiku Bagudu na jihar Kebbi da Gwamna Badaru Abubakar na jihar Jigawa, ne suka yiw zababben gwamnan rakiya  zuwa gaban shugaban kasa, a yayin wata yar kwarya-kwaryar liyafa da aka shirya.

Wata sanarwa da Kakakin Shugaban kasa Femi Adesina ya fitar, Yace Shugaban Kasar ya  yaba dangane da yadda aka gudanar da zaben gwamnan  dama yadda masu zabe da kuma Hukumomin zabe  suka bi  ka’idojin da suka dace wajen yin zaben.

Sanata Adamu , ya Alakanta nasarar da jam’iyyar  ta samu  daga  All..h madaukakin sarki, inda  kuma yayi alkawarin cewa irin abunda zai faru ke nan a yayin zaben gwamna  jihar Osun dake tafe a wata mai zuwa.

More from Labarai