On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Shugaban Kasa Muhammadu Ya Gana Da Wakilan Fasinjojin Jirgin Kasar Da Aka Sace

SHUGABAN KASA BUHARI

Shugaban kasa Muhmmad Buhari ya gana da wakilan wadanda aka yi garkuwa da su a jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna, yayin wani harin da aka kai masa.

Bayanin hakan ya fito ne ta cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin Twitter na fadar gwamanatin shugaban kasa , inda aka bayyana cewa Buhari na  ganawa da wakiln wadanda aka yi garkuwa da su a jirgin kasar.

Yan ta’addan dai suna sako wadanda suka yi garkuwa da su rukuni rukuni, inda na baya bayannan su ne wadanda aka saka a  jiya, inda suka sako mutane 7, da suka hada da mutun shida  yan gida daya, da kuma wata  dattijuwa 1.

Mutane 6 sun hada da mahaifin su mai suna Abdubakar Garba, da matarsa,  Maryam, sai dan su mai shekaru 10 Ibrahim, da Fatima mai shekaru 7, sai Imran mai shekaru 5, da kuma Zainab mai shekara 1 da rabi.

 

More from Labarai