On Air Now

ZANGON SAFIYAR LAHADI

5:00am - Noon

Shugaban Kasa Ya Bukaci Majalisa Ta Amince Masa Ya Ciwo Bashi

BOLA TINUBU

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci zauren majalisar dattawa ta kasa ta sahalle masa ciwo basusuukan kasashen waje domin gaggauta gudanar da wasu aiyukan raya kasa.

Hakan na zuwa ne a yayin da shugaban kasar ya nemi izinin majalisar  wajen amincewa da kwarya-kwaryar kasafin kudin bana na naira tiriliyan 2 da milyan 176, domin aiwatar da Karin albashi na wucin gadi  ga ma’aikata  da kuma gudanar da aiyukan tsaro da sauran wasu aiyuka.

A zaman zaurikan majalisun dokokin kasar  na jiya sun yiwa kwarya-kwaryar kasafin kudin na bana karatu na biyu.

Bugu da kari shugaban kasar ta tura da daftarin tsare-tsaren kashe kudi na  matsaikacin zango daga shekarar 2024 zuwa 2024  ga zaurikan majalisun domin samun amincewarsu.