On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Shugaban Kasa Ya Bukaci Wadanda Aka Karrama Da Lambobin Girmamawa Na Kasa Su Tashi Haikan Domin Hidimtawa Kasa

SHUGABAN KASA BUHARI

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fadawa mutanen da aka karrama da lambar girmamawa ta kasa da cewar ba’a basu ita kawai domin yin ado ba , sai dai domin kara tunasar dasu irin nauyin da ya rataya a wuyansu , a matsayinsu na yan kasa domin cigaba da yin abunda zai amfani Najeriya.

Shugaban ya baiyana haka ne a yayin bukin bada lambobin girmamawa na kasa da aka bawa mutane da sama da 400 a jiya, cikinsu hadda yan kasar waje  Bakwai.

Yace  gina kasa abune dake bukatar sadaukar da kai daga yan kasa, Inda yace irin mutanen da suka bada gudunmuwar su ga cigaban kasa  sun cancanci a yaba masu.

A bisa irin  wannan gudunmuwa da wasu  daidaikun mutane ke bayarwa, hakan tasa ya sake  fasalta kwamitin bada lambobin yabo na kasa a karkashin sarkin Lafiya Mai shari’a Sidi Bage, domin zakulo mutanen da suka dace wajen samun wannan lambobi.