On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Shugaban Kasa Ya Zargi Gwamnoni Da Yin Watanda Da Kudaden Kananan Hukumomi

SHUGABAN KASA BUHARI

Shugaban taraiyyar kasar nan, Muhammadu Buhari, Ya zargi gwamnoni da wawushe kudaden Kananan hukumomin dake jihohin, inda ya danganta irin wannan halaiyya a matsayin ta rashin nagarta.

Shugaban kasar ya yi wannan kalamai ne, a lokacin da yake karbar bakuncin manyan jami’an gwamnati dake daukar horo a cibiyar koyar da dabarun mulki ta kasa karo na 44, a  fadarsa dake Villa Abuja.

Ya  ce abun All…h wadai ne  yadda wasu gwamnonin ke karbar kudaden a madadin  kananan hukumomi  inda suke sakawa  shugabannin kananan hukumomin  dan abunda bai taka kara  ya karya ba.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, Idan kudin da gwamnatin taraiyya ta turawa karamar hukuma naira milyan 100 ne, To  gwamnonin sai su turawa karamar hukumar naira milyan 50 kadai  tare da takardar da zai sa hannu kan cewar ya karbi naira milyan 100.