On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Shugaban Majalissar Wakilai A Najeriya Zai Gana Da Gwamnan Bankin CBN Kan Takaddamar Bangaren Sufurin Jiragen Sama

A ranar Alhamis 20 ga watan Oktoba 2022 ne kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila zai gana da gwamnan babban bankin kasa CBN da kuma ministar kudi.

An dai shirya taron karo na biyu ne kan matsalolin da ake fuskanta a bangaren  sufurin jiragen sama.

Gbajabiamila ya bayyana haka ne a karshen taron da ya yi da masu ruwa da tsaki a harkar sufurin jiragen sama a ranar Litinin a Abuja.

Yace taron an yi shi ne da nufin shawo kan matsalar sufurin jiragen sama.

Masu ruwa da tsaki a taron sun hada da kungiyar masu sufurin jiragen sama ta kasa da kasa IATA da kamfanonin jiragen sama na Najeriya da  hukumomin kula da tafiye-tafiye da sauran masu ruwa da tsaki a harkar sufurin jiragen sama.