On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Shugaban Najeriya Tinubu Na Shirin Balaguro Zuwa Kasar Saudiyya

Shugaban Najeriya Bola Tinubu

Shugaba Bola Tinubu na shirin halartar taron kasashen Larabawa da Afirka da Saudiyya da za a yi a makon nan a birnin Riyadh na kasar Saudiyya.

Mai bada shawara ga  shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai,  Ajuri Ngelale, ne ya bayyana hakan a karshen mako yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.

Ya ce halartar shugaban kasar zuwa taron na cikin  yunkurin gwamnati na amfani da dukkan hanyoyin da za a jawo hankalin masu zuba jari kai tsaye daga kasashen waje zuwa sassa daban-daban na tattalin arziki.

Ngelale ya ce za a yi cikakken bayani a taruka daban-daban da shugaban zai yi da masu zuba jari, wadanda suka shafi farfado da tattalin arzikin kasa.