On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Shugaban Najeriya Tinubu Ya Zama Sabon Shugaban Kasashen Afirka - ECOWAS

Shugaban Kasa Bola Tinubu na Najeriya ya zama sabon shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS.

Tinubu ya gaji Umaro Embalo na Guinea Bissau a matsayin shugaban ECOWAS.

An sanar da zabar Tinubu ne a taron shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS karo na 63 a Guinea-Bissau.

A jawabinsa na farko bayan karbar muhimman bayanai game da shugabancin kungiyar daga shugaba mai barin gado Umaro Embalo, Tinubu ya sha alwashin tabbatar da dorewar mulkin demokradiyya a kasashen yankin.

A cewar sabon shugaban na ECOWAS ya na daga cikin abubuwan da mulkinsa zai bai wa muhimmanci shi ne tabbatar da tafiyar da mulki karkashin demokradiyya da zaman lafiyar kasashe, yana mai cewa wannan batu ne da bazasu dauke shi da wasa ba.

Idan za a iya tunawa ko tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rike wannan mukami na shugabancin ECOWAS daga shekarar 2018 zuwa 2019, lura da yadda ake karba-karba tsakanin kasashe mambobin kungiyar.

Kadan daga cikin nauyin da ke kan duk wani shugaban kungiyar ta ECOWAS shi ne tabbatar da sasanta duk wani rikici da ya taso tsakanin mambobin kungiyar ta hanyar hada kai da shugaban hukumar gudanarwar kungiyar baya ga tabbatar da bin dokoki da tanade tanaden kungiyar tsakanin mambobinta.