On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Shugabannin Majalissa Wakilan Najeriya Zasu Gana Da Shugaba Buhari Kan Yajin Aikin ASUU

Muddin ba’a samu wani sauyi na gaggawa ba, a ranar talata 4 ga watan Octoba shugabannin majalisar wakilai za su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yajin aikin kungiyar malaman jami’oi a kasarnan ASUU.

Wata majiya mai tushe daga fadar shugaban kasa ta fadawa jaridar Punch cewa ‘yan majalisar za su gabatar wa Buhari shawarwarinsu daga ganawar da suka yi da masu ruwa da tsaki kan yajin aikin.

Idan dai ba a manta ba Shugaban Majalisar Wakilai Mista Femi Gbajabiamila ya yi  alkawarin cewa majalisar za ta shirya rahoton kan shiga tsakani da ta cikin takaddamar yajin aikin sannan kuma zata gana da shugaban kasa kan al’amarin.

Shugaban majalisar ya ce rahoton zai nuna yadda suka tattauna da kungiyar ASUU da kuma bayar da shawarwari.

Haka kuma idan za a iya tunawa ministan kwadago Chirs Ngige ya fice daga taron tattaunawa da kungiyar ta ASUU dakayi a makon jiya.

More from Labarai