On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Shugabar NAN A Kano Ta Zama Mataimakiyar Shugabar NAWOJ

Shugabar ofishin kamfanin dillancin labaru na kasa NAN a jihar Kano, Aisha Ahmed ta zama mataimakiyar shugabar kungiyar mata ‘yan jarida ta Kasa NAWOJ reshen Jihar Kano.

Ahmed da wasu mata ‘yan jarida biyar za su tafiyar da harkokin kungiyar na tsawon shekara uku.

Da yake kaddamar da sabbin shugabannin kwamishanan yada labarai, Malam Muhammed Garba, yace ya kamata sabon shugabancin NAWOJ ya cike gibin da ake da shi na  mata ‘yan jarida  a Kano.

Garba ya ce wannan babban kalubale ne kuma ya bukace su da su tashi haikan wajen kawo cigaba.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar ‘yan jaridu NUJ reshen jihar Kano, Malam Abbas Ibrahim, ya bukaci sabbin mambobin kungiyar da su kawar da duk wasu kura kurai a cikin kungiyar sannan su ci gaba da zama tsintsiya madauri daya.

More from Labarai