On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Siyasa Ta Shiga Hukumar Karbar Korafe-Korafe Da Yaki Da Rashawa Ta Jihar Kano - Mallam Shekarau

Tsohon gwamnan jihar Kano Mallam Ibrahim Shekarau ya soki gwamnatocin da suka biyo bayansa akan siyasantar da ukan wasu ma’aikatun gwamnati masu mahinmanci.

Ya bayanawa Arewa Radiyo hakan yayin wata tattaunawa kai tsaye.

Acewarsa daya daga cikin ma’aikatun su ne hukumar karbar korafe-korafe ta jahar Kano wadda aka karkatar da akalar makasudin kafuwarta zuwa musgunawa ta siyasa a jahar.

Shekarau wanda ya kafa hukumar a zamanin mulkinsa ya bayana cewar dalilin kafa hukumar ya samu nakasu daga wasu 'yan siyasa.

"Abun da muka maida hankali shine a tarbiyantar da mutane su daina zalinci, ina murna hukumar ta yi karfi harma hana samun manyan 'kyasa-'kyasai da ake kaiwa duk da dai gaskiya an bari siyasa ta shiga ciki domin duk dambarwar da akeyi kullum shugabanni ana rigima da su kan ko Gwamna ko Sarki bai kamata ba duk wannan bai taso ba, mun kafa wannan hukuma ne domin a samar da masalaha a tsakanin mutane" Inji Shekarau.
Hakazalika ya bayana damuwa akan yadda nadin mukamai da kuma aiyukan hukumar Hisbah shi ma aka siyasantar da shi domin biyan bukatar wasu 'yan siyasan jahar.