On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Sojoji Ba Zasu Karbe Ragamar Mulki A Najeriya Ba, Demukuradiyya Ta Samu Wurin Zama - Irabor

Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Janar Lucky Irabor ya kawar da yuwuwar sojojin  su karbe mulkin Kasar.

Irabor ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a Abuja yayin  kaddamar da fure na bikin tunawa da ‘yan majan jiya.

Yace dimokradiyya ta zo ta samu wurin  zama kasarnan.

Yanzu haka dai sama da ’yan wasan kwallon gora  250 da suka ƙunshi ƙwararru da ’yan wasa masu sha’awa da mata da manyan jami’an gudanarwa da duk masu ruwa da tsaki a harkar  tsaro sun halarci wasannin gasar tunawa da dakarun sojojin  a bana.

Iraborn ya kara da cewa gasar tana da matukar muhimmanci ga rundunar sojin kasarnan domin ta baiwa sojoji damar tunawa da jarumtar ‘yan mazan jiya da suka mutu  da kuma wadanda suke raye.

More from Labarai