On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Taiwo Awoniyi Na Cikin Masu Takarar Gwarzan Dan Wasan Premier Na Watan August

AWONIYI

Dan wasan Super Eagles, Taiwo Awoniyi ya kasance cikin jerin sunayen ‘yan wasanda da aka zaba domin takarar gwarzon dan wasan Premier na watan Agustan bana.

Dan wasan na  kungiyar kwallon kafa ta  Nottigham Forest ya zira kwallaye uku a wasanni hudu da ya buga wa Forest, wanda ya kara nuna  bajintarsa  ta iya  tamaula.

Sanarwar da aka fitar  a jiya, ta baiyana cewar  an zabi   ‘yan wasa shida domin takarar  kanbun  gwarzon dan wasan na watan  Augusta.

Dan  wasa  Awoniyi ya tsawaita yawan zura kwallo a raga tun daga kakar wasan da ta gabata zuwa wasanni bakwai a jere a gasar Premier, wanda shi ne dan wasan Afrika na uku da ya yi hakan.