On Air Now

ZANGON SAFIYAR LAHADI

5:00am - Noon

Takardar kudi ta Naira ta samu tagomashi a kasuwar chanji

Naira Dari 4 da 16 da Kobo 62 a ranar Talata

An canzar da takardar kudi ta naira kan 416 da kobo 62 akan kowace Dala  1 a ranar Talata a kasuwannin ‘Yan canji, wanda  hakan ya nuna cewa takardar nairar ta ‘dan samu tagomashin kobo 9 akan kowace Dala 1 idan aka kwatanta da yadda aka yi musayarta Ranar Litinin, akan naira  417  kan kowace Dala guda.

Rahotanni sun baiyana cewa  Darajar takardar  Dalar sai da ta kai har naira  Dari 4 da 44  kafin  daga bisani ta sauka zuwa  Naira Dari 4 da 16 da Kobo 62 a ranar Talata.

Gabaki daya jimillar kudaden musayar da aka yi canjinsu a ranar Talata  kadai, ya kai Dala Milyan 127 da Da dubu  12.