On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Tallafin Karatu : Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafi Ga Masu Karatun Digiri A Fannin Ilmi Da Kuma Masu NCE

Gwamnatin tarayya ta bude shafi ga daliban da suka cancanta da ke karatar bangaren Ilimi a Jami’o’i da kwalejojin ilimi domin neman tallafin Karatu.

Idan za a iya tunawa, a yayin bikin  tunawa da ranar malamai ta duniya da aka gudanar a Abuja a shekarar da ta gabata, gwamnatin tarayya ta ce daliban da ke karatun digiri a fannin ilimi a jami’o’in gwamnati za su samu tallafin Naira dubu 75 a kowabne zangon karatu, yayin da takwarorinsu masu karatun NCE za su samu   Nairandunun 50 kowane zango.

A wata sanarwar manema labarai da babban sakatare a ma’aikatar ilimi ta tarayya, Andrew David Adejo, ya fitar, gwamnatin ta ce a yanzu ana samun fom din a Internet  yayin da wa’adin cikewa  ya kasance 21 ga watan Oktoba na 2022.

Ya ce ka’idojin cancantar bayar da tallafin karatun sun hada da masu  karatu a kwalejojin ilimi da jami’o’in Najeriya kuma masu neman cin moriyar dole ne su zama dalibai dake karatu na cikakken lokaci (Full-time)