On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Tanko Muhammad Ya yi Murabus A Matsayin Alkalin-Alkalai

Alkalin Alkalai na kasa Mai Shari'a Ibrahim Tanko Muhammad ya yi murabus daga kan mukaminsa.

 

Mai taimaka ma sa na musamman kan harkokin yada labarau Isah Ahuraka shine ya tabbatar da hakan ga manema labarai da safiyar yau Litinin.

 

Kafin Ajiye mukamin rahotanni sunce Tanko na fama da rashin lafiya mai tsanani.

 

Sai dai ana hasashen murabus din nasa na da alaka da rikicin da ke faruwa tsakaninsa da manyan alkalan Najeriya 14 wadanda a makon jiya suka zarge shi da rashin iya shugabanci.

A watan Janairun 2019 ne shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya rantsar da Mai Shari'a Ibrahim Tanko Muhammad a matsayin mukaddashin Alkalin Alkalan kasar bayan dakatar da Alkalin Alkalan wancan lokaci, Walter Onnoghen bisa zargin da ya shafi kin bayyana kadarorin da ya mallaka.

 

 

More from Labarai