On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Tinubu, Atiku, Obi Da Kwankwaso Na Cigaba Da Zafafa Yakin Neman Zabe A Najeriya - 2023

Yayin da ‘yan Najeriya ke kidayar sauran kwanakin da suka rage a gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 25 ga watan Fabrairu, ‘yan takarar shugabancin kasar na ci gaba da zafafa yakin neman zabe.

A jiya ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya sha alwashin cire kudaden tallafin man fetur a Najeriya ranar farko idan aka zabe shi amatsayin shugaban kasa.

Obi ya bayyana haka ne a gidan talabijin na Channels.

Tsohon gwamnan jihar Anambra ya bayyana biyan tallafin man fetur a matsayin laifi, inda ya ce babu wata kasa mai sanin ya kamata da za ta kashe kudaden tallafi fiye da ilimi da  kayayyakin more rayuwa da  lafiya da dai sauransu.

Shi kuwa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya kudurinsa na cika alkawuran yakin neman zabensa idan har aka zabe shi a matsayin shugaban Najeriya a babban zaben da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Dan takarar na jam’iyyar APC ya bayyana haka ne a jiya a wani gangamin nuna goyon baya da ‘yan Arewa suka shirya a Legas, inda ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta kasance ga daukacin ‘yan Najeriya ba tare da la’akari da kabilarsu ko addininsu ba.

Tinubu ya kuma yi alkawarin tunkarar kalubalen tsaro da ake fuskanta a fadin kasar nan, inda ya bayyana cewa tattalin arzikin kasa ba zai iya bunkasa a cikin yanayi na rashin tsaro ba.