On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Tinubu Bai Halarci Taron Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Tsakanin Yan Takarar Shugaban Kasa

Bola Ahmed Tinubu

Ba'a fuskar Dan Takarar Shugaban Kasa na Jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ba, A yayin taron kwamitin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin Yan takara a lokacin yakin neman zabe ba.

An dai yi taron ne a Abuja babban birnin taraiya, karkashin tsohon shugaban kasa na Mulkin soja janar Abdulsalam Abubakar mai ritaya.

An ga fuskokin 'yan takara kamar na jam'iyyar Labour, Peter Obi da mataimakin dan takarar jam'iyyar APC Kashim Shettima Wanda ya wakilci Tinubu da Atiku Abubakar, dan takarar jam'iyyar PDP. 

Sauran 'yan takarar sun hadar da na jam'iyyar NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso da Hamza Al-Mustafa na jam'iyyar AA, akwai Omoyele Sowore na jam'iyyar AAC.

Wasu rahotanni da ba'a tabbatar ba na cewa tunubun baya cikin Najeriya, inda wasu ke rade rade radin yana Burtaniya.