On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Tinubu Ya Ce Bashi Da 'Dan Takarar Da Yake Son Ya Zama Shugaban Majalisa

Bola Tinubu

Kalaman nasa na zuwa ne a yayin da wasu daga cikin Yan majalisar ke cigaba da kamun kafa domin ganin sun dare kan shugabancin majalisun dokoki ta kasa.

Zababben Shugaban kasa, Bola Tinubu ya ce bashi da wani  ‘Dan takara  da yake muradin ya zama  shugaban majalisar dattawa  kota wakilai a zauren majalisun na 10  da za’a kaddamar nan gaba  kadan.
Tinubu ya baiyana haka ne a yayin ganawarsa da sabbin  zababbun  ‘yan majalisar dokoki  ta kasa  a ranar Litinin, Kamar  yadda mataimakinsa  Kashim Shettima  da  ya wakilce shi a wajen taron ya   baiyana.
Wani zababben dan majalisar wakilai dake  wakiltar  Bungudu da Maru  daga jihar Zamfara, Abdulmalil Bungudu ne ya  baiyana haka jim kadan bayan kammala taron.
Dan majalisar  ya baiyana cewar, Zababben shugaban kasar  ya  baiyana cewa  bashi da wani dan takara  da yake  muradin ya  zama wani  jagoraa cikin sabbin zaurikan majalisun na kasa  da za’a kafa.