On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Tinubu Ya Jinjinawa Tawagar Super Eagles

TINUBU

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tawagar ‘yan wasan Najeriya ta Super Eagles murnar nasarar da suka samu akan kasar Afrika ta Kudu, a wasan kusa da na karshe na gasar cin Kofin nahiyar Afrika da suka buga a daren jiya.

Super Eagles  ta doke kungiyar kwallon kafa ta Bafana-Bafana da ci 4 da 2 a bugun daga kai sai mai tsaron gida, Bayan  tashi wasan ana ci 1 da 1, duk da karin lokacin da aka yi, a wasan da suka buga a kasar Coted’Ivoire.

Dan wasa Kelechi Iheanacho ne  ya ci kwallo ta karshe a bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan da mai tsaron gidan Najeriya Stanley Nwabali  ya tare kwallaye biyu a bugun daga kai  sai mai tsaron raga, wanda hakan yasa Najeriya ta kai wasan karshe na gasar.

Da yake tsokaci kan nasarar da kungiyar ta samu a shafinsa na X, Shugaban kasa Tinubu ya jinjinawa kungiyar ta Super Eagles saboda nasarar da suka samu,  tare da kara jan hankalinsu akan su jajirce domin ganin sun samu nasara a wasan karshe  na gasar.