On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Tinubu Ya Shiga Tsakani Kan Yunkurin Tsige Gwamnan Jihar Ribas

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu tare da jam’iyyar PDP sun shiga tsakani domin ganin sun dakile yunkurin tsige gwamnan jihar Ribas Sim Fubara.

 

Kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP ta yi maraba da matakin  shiga tsakani da shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi akan  rikicin siyasar  jihar Ribas, inda ya yi kira ga bangarorin da  takun saka da juna, dasu maida wukar  cikin kubenta.

Bayanin hakan na kunshe ne  cikin wata sanarwar da gwamnonin suka fitar a yammacin jiya Talata bayan sun gana a masaukin gwamnan jihar Oyo da ke Abuja inda suka tattauna kan rikicin siyasar  jihar Ribas  mai arzikin man fetur da sauran wasu  batutuwan da suka shafi  kasa.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya bayyana cewa Gwamnonin PDP sun damu da irin abubuwan dake faruwa  a jihar Ribas,  kuma sun yi maraba da matakin sasanta rikicin da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi.

Taron ya bukaci dukkan bangarorin da ke rikici da juna a jihar Ribas da su  yi amfani da hanyoyin masalaha wajen  warware rikicin cikin lumana.

Taron  gwamnonin na PDP a jiya Talata, ya biyo bayan rikicin siyasar da barke a jihar, wanda  ta kaiga majalisar dokokin jihar  ta  yi yunkurin tsige Gwamna Sim Fubara, daga kan kujerarsa.