On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Tinubu Ya Zabi Mataimaki

Dan Takarar Shugaban kasa a karkashin Jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Ya Zabi Kabiru Masari a matsayin Wanda zai y masa takarar Mataimaki.

Wani Kusa a jam'iyyar APC, Kabiru Faskari ne ya tabbatar da haka yayin zantawarsa da gidan Talabijin na Channels a Ranar Juma'a.

Ya Kara da cewa, Alhaji Kabiru Masari ya taba rike matsayin Sakataren Walwala na jam'iyyar APC, a zamanin Adams Oshimole.

Kazalika ya baiyana Kabiru a matsayin Mutum Mai 'kana'a da Kusanci na musamman ga Bola Tinubu, Wanda ba zai watsa masa kasa a fuska ba.

More from Labarai