On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Tinubu Ya Zolayi Atiku Kan Yadda Ya Jima Yana Neman Mulkin Najeriya

TINUBU DA ATIKU

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya taya abokin karawarsa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar murnar cika shekara 76 a duniya a ranar juma’a.

Tinubu ya aike da sakon taya murnar ne a shafinsa na Twitter, Yan sa’oi bayan ya zolayi Atiku Abubakar, kan yunkurin da yayi tayi domin zama shugaban kasa, a yayin wani taron masu ruwa da tsaki na yankin Naija Delta.

Bugu da kari  Bola Tinubu ya sake yin gugar zana kan wani dan takarar shugaban kasa, wanda bai ambaci sunansa ba, amma wasu mutanen na kallon cewar, da Peter Obi na jam’iyyar Labour  yake.

A wani bangaren kuma, Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi ya taya abokin hamaiyarsa a zabe mai zuwa, Atiku Abubakar  murnar  cika  shekara  76 da haihuwa.

A wani sako da ya wallafa,  Peter  Obi, Yace  yana  taya  yayansa Alhaji Atiku Abubakar Murnar  cika shekara 76 a duniya,  Allah daya sa ka kawo wannan lokaci, ya albarkaci rayurka  a kowane lokaci, Barka da zagoyowar ranar  Haihuwarka  ranka ya dade.

Idan ba’a manta ba, Peter Obi shine yayi wa Atiku takarar mataimakin a zaben shugaban kasa na shekarar 2019.