On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Tsadar Taki Tasa Manoma A Kano Yin Amfani Da Gishiri Da Kanwa Wajen Yin Noma

KANWA DA GISHIRI

Tashin gwauron zabi da farashin takin zamani yayi a kasar nan, Ya tilastawa manoma a nan jihar Kano yin amfani da Gishiri da kuma kanwa wajen yin nomansu.

Wasu manoman sun baiyana cewa, a baya suna amfani da gishiri da kanwar ne kawai  domin  kara inganta takin, to amma a bana abun yasha banban, inda suke amfani dasu kadai wajen yin nomansu.

To sai dai kuma masana sunyi gargadin cewa yin amfani da wannan hanya zai illa  ga kasar da ake noma a kanta, inda suka  bada shawarar yin amfani da takin gargajiya.

A yanzu haka dai  farashin takin zamanin ya haura dubu 25 inda a wasu ke yake kaiwa har kusan dubu 30.

Tsadar takin na zuwa ne a yayin da gwamnati ke ikirarin  bijiro da shirye-shiryen  bunkasa aikin gona da kuma tallafawa manoma a Najeriya.

More from Labarai