On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Tsaffin Jami'an Yansanda Sunyi Zanga-zanga A Kano.

JAMI'AN YANSANDA

Jami’an Yansandan da suka yi ritaya, wanda ke karkashin tsarin temake-keniyar biyan fanso, sunyi wata zanga-zangar lumana a nan kano, bisa abunda suka baiyana na tsantsar rashin adalci da ya daibaibaye tsarin biyan fanshon.

Jim kadan  bayan wani taron koli na gaggawa da suka gudanar a filin wasa na Sani Abacha dake nan Kano, Tsaffin Jami’an Yansandan  sun gabatar da zanga-zangar lumana, inda suka rika kokawa kan yadda  hukumar kula da biyan fansho ke tafiyar da tsarin temakekeniyar  biyan fansho na kasa.

Jagoran masu  zanga-zangar, wanda kuma shine  shugaban kungiyar tsaffin jami’an yansanda a nan Kano, Yunusa Yahaya Madaki, Yayi zargin cewa, hakkokinsu na fansho da kuma  gratuity  ana karkarkatar dasu ne kawai zuwa ga wata biyan bukata  ta kashin kai.

 

 

More from Labarai