On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

UTME 2022: Hukumar JAMB Zata Karbi Korafin ‘Dalibai

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta kasa JAMB reshen jihar Kano, tayi kira ga ‘Daliban da sukayi rijista amma ba su rubuta jarabawar UTME ta bana ba, dasu kai korafinsu ga ofishin Hukumar dake a yankin Farawa a karamar Hukumar kombotso.

Hakan  dai  na  zuwa  ne  bayan  samun  korafe-korafe  da  dama  daga  ‘Daliban  da  sukayi  Rajista  domin  Rubuta  jarabaawar, wadanda  basu  samu  Damar  Rubutawa ba  kamar  yadda  aka  tsara  a  sakamakon  kura-kurai  da  suka  hadar  da   matsalolin  internet  da  matsalar Dangwalen  yatsa  da  kuma  na  Na’urar  tantancewa  a wasu cibiyoyin  Rubuta  jarabawabar.

Wani  babban  jami’in  hukumar  da ya  Bukaci  a  sakaya  sunansa  ya  yiwa wakiliyarmu  Joy Godson  karin  haske ,  inda  yace  Hukumar  ba zata  lamunci  kowanne  irin  korafi  daga  ‘Daliban   da  suka ki zaunawa jarabawar a lokacin  daya  kamata  su  Rubuta  ko  kuma  wadanda  suka isa  cibiyoyin  jarabawar  a makare.

Sai dai  ya yi fatan  cewa   dai  Hukumar  JAMB zata  yi  nazari  kan  ‘Daliban  da  abun  ya  shafa  domin  yin  abun da ya  da ce.