On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Wahala Da Kuncin Rayuwa Sun Addabi Mafi Yawan Jama'a, Hakkin Samar Da Mafita Na Kan Shugabanni - Zaure

Zauren hadin kan Malamai da kungiyoyin Musulunci na Jahar Kano ya ce yana jajantawa al'umma game da halin da aka sake tsunduma a ciki a Najeriya, na karancin man fetur da kuma tsada da ya yi.

Sanarwa da aka aikowa Arewa Radio na dauke da sahannun  Dr, Saidu Ahmad Dukawa Sakataren Zauren.

Ga cikakken bayanin sanarwar mai sadara guda 9.

 

1.  Zauren hadin kan Malamai da kungiyoyin Musulunci na Jahar Kano ya na jajintawa Alumma game da halin da a ka sake tsunduma a ciki a Kasa, na karancin man fetur da kuma tsada da yayi.

2.  Babu shakka an shiga wani mawuyacin hali, musamman a irin wannan yanayi da ake ciki na tsananin zafin rana da karancin wutar lantarki.

3.  Zaure yana jan hankalin shugabanni da su gaggauta daukan dukkanin matakan da suka dace domin samar da rahama da jinkai da saukin rayuwa ga al'umma

4.  Hakika wahala da kuncin rayuwa sun addabi mafi yawan jamaa, kuma hakki ne a kan shugabanni su samar da mafita.

5.  Zaure ya na jan hankalin Shugabanni da su yi la'akari da gargardi da Manzon Allah SAW ya yi da kuma narkon da ya ambata game da duk wanda ya jibinci al'amarin a'umma. amma ya tsananta ma su.

6.  Zaure kuma ya na jan hankalin Shugabanni da duk wanda su ke da hannu a cikin masa'alar man fetur, da su ji tsoron Allah akan wannan al'amari. Allah cikin falalarSa da ni'imarSa Ya azurta kasarmu da man fetur, bai kamata ya zama hanyar azabatar da alumma ba.

7.  Zaure ya na jinjina ga alumma game juriya da hakuri da su ke yi a irin wannan hali, babu shakke shakka sauki zai biyo bayan tsanani

8.  Don haka Zaure ya na kira ga galumma su dage da adduar neman taimakon Allah, ya magance duk abinda ya fi karfin su, kuma ya yi ma su maganin duk wanda ke da hannu wajen gallaza ma su.

9.  A karshe, Zaure ya na kira ga Malamai da limamai a kan su ci gaba da fadakarwa da adduoi da suke yi na neman sauki daga Allah, domin fita daga kangin wahala da a ka tsinci kai

Allah Ya bamu lafiya da zaman lafiya a kasarmu baki daya.