On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Wane Hali Shari'ar Zaben Gwamnan Jihar Kano Na 2023 Ke Ciki ?

Gwamna Kabir Yusuf na jihar Kano ya rufe kare kansa daga karar da  jam'iyyar APC ta shigar inda ya gabatar da sakataren gwamnatin jihar Kano  Dr Abdullahi Baffa-Bichi a matsayin shaida daya tilo.

A zaman Kotun Sauraran karararkin zaben Gwamnan Karkashin me Shari'a Justice Akintan Osadebay Lauyan Gwamna Abba Kabir Yusuf Eyitaye Fatugun SAN, ya gabatar da Dr Abdullahi Baffa Bichi a matsayin Shaidarsu na kariya da suka rufe da shi.

Kafin gabatar da shari'ar APC sun gabatar da sakamakon zabe na wasu kananan Hukumomi ciki harda Karamar hukumar Bichi.

Jam’iyyar APC na kalubalantar Hukumar Zabe ta kasa INEC kan ayyana Abba Kabir  Yusuf na Jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Jihar da aka gudanar a ranar 18 ga Maris.

Baffa Bichi ya shaidawa kotun cewa INEC ta bayyana Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben a ranar 20 ga watan Maris, bayan da ya samu kuri’u milliyan 1 da dubu 19 da 602 yayin da Nasiru Gawuna na APC ya samu kuri’u dubu 890 da 705, da tazarar kuri’u dubu 128 da 897.

Bichi ya amsa tambayoyi daga Lauyan Jam'iyyar APC, Effion Effion  SAN cewa wace irin rawa ya taka, sai Baffa ya ce, ya je hukumar zabe ne a matsayin wakilin NNPP na Jihar Kano.

Baffa ya bayyanawa Kotun cewa ya je INEC  ya tabbatar sun bi dokokin kundin tsarin mulkin kasa dana Hukumar zabe, yayin ayyana sakamako, ya kuma gamsu da yadda Hukumar zabe ta gabatar da aikinta.

Bayan kammala bada Shaidarsa Kotun ta dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar litinin 24 ga watan Yuli 2023, domin bangaren da ake kara na uku Jam'iyyar NNPP su kawo shaidunsu ta kariya.