On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Wani Dan Bindiga Ya Bude Wuta A Kasar Amurika

AMURIKA

Jami’an Yansandan Kasar Amurika, Sun dakume wani mutum da ake zargi bayan harbe wasu mutane 6 a yayin wani harbin kan mai uwa da wabi da aka yi, lokacin da ake wani faretin tunawa da ranar samun yancin kai, wani wurin shakatawa na Highland dake Illinois.

Jami’an Yansanda sun baiyana cewa, Wanda ake zargin dan shekara 22 a duniya mai suna Robert  E Crimo, Ya haura zuwa saman wani rufi, inda ya rika yin harbin kan mai uwa da wabi a wajen da mutanen suka taru.

Yan sa’oi bayan faruwar lamarin ne,Aka samu wasu Jami’an yansanda biyu dauke da raunika a Philadelphia, a yayin wani wasa da wuta karo na hudu da ake yi a cikin watan yuli.

Wannan shine  harin bindiga  na kwanan nan da aka fuskanta a kasar Amurika, a yayin da ake samun  kai hari kusan kowanne  mako a shekarar bana.

 

More from Labarai