On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Wani Farfesa Ya Bukaci Tinubu Ya Nunawa Duniya Sakamakon Gwajin Lafiyarsa Bayan An Duba Shi

BOLA TINUBU

Wani masanin Siyasar Tattalin Arziki, farfesa Pat Utomi ,Ya kalubalanci Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da yaje a duba lafiyarsa, Sannan kuma ya nunawa duniya sakamakon binciken da aka yi masa.

A yayin hirarsa da gidan  Talabijin  na Channels  a daren jiya, Pat Utomi ya yi ikirarin cewa , Dan takarar shugabancin kasar na jam’iyyar APC bai dace da jan ragamar  shugabancin kasar nan ba.

Ya kara da cewa akwai  tarin alamu da suke nuna   cewa  Tinubun bai dace  da wannan matsayi ba.

A cewar Farfesan,  Shugabannin Kasar Amurika suna zuwa a duba lafiyarsu sannan kuma su nunawa jama’a sakamakon gwajin da aka yi masu, a saboda haka ne ya bukaci  Tinubu da  ya dauki irin wannan mataki.

More from Labarai