On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Wani Gari Ya Biya Milyan 20 Domin Kaucewa Harin Yan Bindiga A Jihar Zamfara

Bello Turji

Mazauna kauyen Gidan-goga da ke karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara sun biya harajin Naira miliyan 20 da shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji ya dora musu domin dakile hare-haren da ake kai wa al’ummarsu.

Turji, wanda ya dorawa mazauna kauyen harajin Naira  milyan  20   2m, ya bukaci su biya kudin ko kuma kafin ranar Lahadin data  gabata  27 ga watan Nuwamba,  su fuskanci fushinsa, inda ya yi barazanar kai hari ga mutanen kauyen bayan karewar  wa’adin.

Wani dan yankin da ya nemi a sakaye sunansa ya bayyanawa manema labarai cewa an biya kudin ne a ranar Lahadi. Majiyar ta ce bayan biyan kudin, wasu mazauna garin da suka gudu zuwa wasu wurare, sun fara komawa gida.

Har yanzu dai rundunar ‘yan sandan jihar ba ta ce uffan ba kan sabon lamarin.

More from Labarai