On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Wani Jirgin Dakon Kaya Yayi Hadari A Kasar Girka

HOTON HADARIN JIRGIN SAMA

Wani jirgin dakon kaya ya yi hadari a kusa da birnin Kavala da ke arewacin kasar Girka.

Jirgin mai suna Antonov-12  mallakin wani kamfani da ke Ukraine ya taso ne daga Sabiya zuwa Jordan a lokacin da ya  rikito a jiya. Kawo yanzu Ba a kaiga sanin  adadin mutanen da ke cikin jirgin, ko  kuma sanin  wadanda suka tsira.

Rahotanni sun baiyana cewa  matukin jirgin ya yi kokarin yin  saukar gaggawa a filin jirgin Kavala saboda matsalar  da  injin jirgin ya samu amma jirgin ya kasa isa titin jirgin.

Mahukuntan yankin   sun ce an tura motocin kashe gobara bakwai amma ba su iya tunkarar wurin da hadarin ya  faru  ba, saboda yadda jirgin ke cigaba da tarwatsewa a lokacin.

 

More from Labarai