On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Wani Lauya Ya Bukaci Kotu Ta Ayyana Kujerar Ekweremadu Amatsayin Wadda Babu Kowa Tare Da Sanya Sunansa Amatsayin Wanda Zai Maye Gurbin Sanatan

Wani Lauya Mazaunin jihar Enugu, Ogochukwu Onyema ya garzaya babbar kotun tarayya dake zamanta a jihar, inda ya Roki kotun data ayyana kujerar mazabar Enugu ta yamma amatsayin babu kowa tare da sanya sunansa amatsayin wanda zai maye gurbin sanatan.

Tsohon  mataimakin  shugaban  majalisar  dattawa,  sanata  Ike  Ekweremadu  shine  sanata  dake  wakiltar  wannan  mazaba  ayanzu  haka  wadda  kuma  ta  kasance  mahaifar  Lauyan

Onyema  ya  Bukaci  kotun  data  ayyana  kujerar  amatsayin  babau  kowa,  asakamakon    cigaba  da  tsare   Dana  majalisar  a  kasar  Burtaniya,  inda  ake  tuhumarsa  da  alaifukan  da  suka  Danganci  safarrar  sassan  jikin  Dan ‘adam ,  Acewar  Onyeama  bai  kamata  acigaba  da  barin  kujerar  babu  kowa  ba  ayyainda  Ekweremadu  ke  tsare

A shari’ar da aka shigar a babbar kotun tarayya, Enugu, Onyema ya kuma roki kotun data bada umarni da kuma baiwa shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu da jam’iyyar PDP su zabi, tare da mika sunansa ga Majalisar   Dokoki  ta  kasa a matsayin wanda   zai maye gurbin Ekweremadu.

Hakazalika  ya kuma roki kotun data umarci Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa Farfesa Mahmood Yakubu da Hukumar  ta INEC    su  janye  ko soke takardar shaidar cin zabe a baya da aka baiwa wanda ake kara na 3 (Ekweremadu)  tare mika  masa  Shaidar  cin  zaben