On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Wani Sabon Rikici Ya Sake Barkewa A Jam'iyyar PDP Biyo Bayan Dakatar Da Kusoshinta

Gwamna Nyesom Wike na Rivers ya kalubalanci  dakatarwar da aka yi wa Ayo Fayose da wasu ‘yan jam’iyyar PDP.

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose ya bayyana dakatarwar da akayi ma sa  daga jam’iyyar PDP da kwamitin gudanarwa  na jam’iyyar na kasa ya yi a matsayin Ihu bayan hari.

PDP ta sanar da dakatar da Fayose da  tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim da Farfesa Dennis Ityavyar da Aslam Aliyu a ranar Alhamis bisa zargin yiwa  jam'iyyar zagon kasa.

Da yake mayar da martani, Fayose ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Lere Olayinka, ya bayyana dakatarwar da kwamitin gudanarwa karkashin jagorancin Sanata IyorchiaAyu ya yi ma sa amatsayin Ihu bayan hari..

Ya ce shi da sauran wadanda suka tsayawa jam’iyyar a lokacin da Ayu da ‘yan tawagarsa suka bar jam’iyyar ta  mutu za su kwato PDP su sake dawo da ita hayyacinta a lokacin da ya dace.

Jam’iyyar ta dakatar da Fayose da sauran wasu jiga-jiganta  a ranar Alhamis sannan ta bukaci Gwamna Samuel Ortom na Benue da ya gurfana a gaban kwamitin ladabtarwa kan wannan zargin zagon kasa.

Da yake mayar da martani a daren jiya, Wike ya ce jam’iyyar PDP  da ke karkashin Iyorchia Ayu ba zata iya dakatar da mambobinta ba saboda shi Ayu akwai irin wannan zargi akansa lokacin da jam’iyyar ta yi watsi da batun tsarin karba-karba karkashin shugabancinsa.

Wike ya ce Ortom ba zai bayyana a gaban kwamitin jam'iyyar ba.

Yace zuwan  gwamna ga kwamitin ladabtarwa na kasa zai kasance gagarumin cin fuska wanda ba zasu lamunta ba.