On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Wasu 'Yan Kasuwa Sun Bukaci CBN Ya Tilastawa Bankuna Bayar Da Sabbin Takardun Kudi Na Naira

‘Yan kasuwa a jihar Anambra sun bukaci babban bankin kasa CBN da ya tilastawa bankunan kasuwanci akan samar da sabbin takardun kudi na naira da aka sake fasaltawa a rassa daban-daban domin a samu saukin kawar da tsofaffin takardun kudi.

Babban bankin ya tsara cewa kudin Naira 200 da Naira 500 da kuma Naira dubu 1 da ake amfani da su a halin yanzu, za su daina aiki bayan 31 ga wannan watan na Janairu.

Sai dai bincike da aka gudanar  a na’urorin ATM da ke bankuna daban-daban, ana ci gaba da bayar da tsofaffin takardun duk da ikirarin da CBN ya yi na baiwa bankunan kasuwanci sabbin takardun kudin.

A wani shirin wayar da kan jama’a game da canza kudaden da aka yi a babbar kasuwar Onitsha, shugaban ‘yan kasuwar  Innocent Ezeoha, ya ce ‘yan kasuwar a shirye suke su bi wannan umarni, sai dai yace babban kalubalen shi ne rashin samun sabbin takardun a bankunan kasuwanci.

A wani bangaren kuwa, bankin CBN ya zuba dala biliyan 15.3 cikin tattalin arzikin kasarnan domin daidaita darajar Naira daga watan Janairu zuwa Oktoba na shekarar 2022.

An samu wannan bayani ne a cikin rahoton tattalin arziki na wata-wata da na zango a bangaren banki da kasuwar canji.

Rahotanni sun bayyana cewa an shigar da dala biliyan 4.86 da dala biliyan 4.81 da kuma dala biliyan 4.18 a cikin rubu'i na farko da na biyu da na uku, yayin da aka sanya dala billiyan  1.46 a watan Oktoba.

More from Labarai