On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Wata Daliba Daga Jihar Sokoto Ta Samu Maki Sama Da 200 A Jarabawar Shiga Karamar Makarantar Sakandire

Gwamnatin Taraiyya ta Fitar da Sakamakon Jarabawar Shiga Karamar Makarantar Sakandire Na Makarantun Gwamnatin Taraiyya Na Hadaka.

Magatakardan  Hukumar  Rubuta  Jarabawar Kammala Makarantun Sakandire ta kasa, Farfesa Dantani Wushishi ne ya  gabatar da Sakamakon Jarabawar  ga Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu a Abuja.

Ministan wanda ya samu wakilcin  Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi ta kasa, David Gender, Yace Iyayen Dalibai zasu iya duba sakamakon jarabawar yaransu ta  hanyar shiga adireshin, WWW.NECO.GOV.NG domin ganin sakamakon jarabawar.

Ya kara da cewa wata Mai suna Mariam Akanke yar asalin jihar Sokoto  it ace  tafi  samu maki a  wadanda suka rubuta  jarabawar, inda  ta samu  202, Yayin da Obot Abundance Idara daga jihar  Akwa Ibom  Tazo ta biyu  bayan data samu maki  200.

More from Labarai