On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Wata Kotu Ta Umarci Gwamnatin Najeriya Ta Mayar Da Jagoran Kungiyar 'Yan Aware Na Biafra Nnamdi Kanu Kasar Kenya

Wata kotu ta umurci gwamnatin Najeriya ta mayar da shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra IPOP Nnamdi Kanu ZUWA kasar Kenya inda ta dauko shi ba bisa ka’ida ba.

Mai shari’a a kotun tarayya dake birnin Umuahia, Evelyn Anyadike itace ta gabatar da wannan hukunci, yayin da ta bukaci gwamnatin tarayya ta biya Kanu diyyar naira miliyan 500 saboda take ma sa hakki.

Lauyoyin Kanu suka shigar da kara a kotun inda suke neman a bi musu hakki akan kama shi da jami’an gwamnatin tarayya suka yi a kasar Kenya ba bisa ka’ida ba da kuma tiso keyarsa zuwa Najeriya, bayan ya karya sharadin bele tare guduwa.

Mai shari’a Anyadike tayi nazari akan hukuncin kotun daukaka kara da ta saki Kanu a Abuja ranar 13 ga watan Octoba wajen amincewa da bukatun guda 8 wadanda suka kunshi biyan diyyar da kuma mayar da shi kasar Kenya inda aka kama shi.

Anyadike ta ce, yadda aka kama Kanu aka ci zarafinsa da tsare shi da kuma kin bada shi belinsa ya nuna karara yadda aka take hakkinsa.

Lauyan Kanu, Alloy Ejimakor ya jinjinawa mai shari’ar akan wannan hukunci wanda yace ya tabbatar da zaman kotu a matsayin wadda ke kare hakkin wadanda aka zalunta.

Har ila yau, lauyan ya bukaci gwamnatin Najeriya ta mutunta hukuncin kotun.