On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Wata Mai Tsohon Ciki Ta Haifi Santalelen Jariri A Hannun Yan Bindiga A Jihar Kaduna

MASU GARKUWA DA MUTANE

Wata mata mai tsohon ciki da yan bindiga suka sace a cikin watan Yulin Bana a Mando dake jihar Kaduna, ta haifi santalelen jariri a wurin da ‘yan bindigar suke tsare da ita.

Rahotanni sun baiyana cewa matar ta fada komar  yan bindigar ne akan hanyarta ta zuwa  duba  mahaifiyarta dake fama da rashin lafiya , inda aka sace ta tare wasu  yan uwanta mata biyu.

Da yake tsokaci kan al’amarin, Mijin matar mai suna Mohammed Alabi, Yace mai dakin nasa ta haihu a hannun masu garkuwar a ranar  Biyu ga watan Augustan bana, kuma  babu wata kulawa da mai jegon tare da jaririn suka samu.

Alabi ya koka  kan yadda  yadda masu garkuwar ke azabtar da iyalin nasa, inda yace  da farko sun nemi a basu naira milyan 140 kafin daga bisani su mayar da ita zuwa naira  Milyan 50.

 

 

 

More from Labarai