On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Ya Zama Dole Jam’iyyun Adawa Su Hade Kan su Domin Kubutar da Najeriya – Atiku

Atiku Abubakar, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya sake jaddada bukatar dake da akwai wajen hadin kan jam’iyyun adawar kasar nan domin kawo karshen gallazawa ‘yan kasa da jam’iyyar APC ke yi.

Atiku, wanda jigo ne a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, ya bayyana hakan ne yayin da gamayyar kungiyoyi dake karkashin jam’iyyar PDP ta kasa, suka kai masa ziyarar ban girma a gidan sa domin sake jaddada goyon bayan su a gare shi.

Da yake Magana a madadin kungiyoyin, shugaban tawagar Engr. Anuca Katchy ya ce sun gamsu cewa Wazirin Adamawan na da dukkan abubuwan da ake bukata wajen ciyar da kasar nan gaba, la’akari da yadda ya yi fice wajen sanya kishin kasa a gaba da komai da kuma irin cigaban da ya samar lokacin da yake gwamnati.

Katchy, ya tunasar da tawagar cewa Atiku ne ya jagoranci yarjejeniyar da ta yafe wa Najeriya bashin nan na Paris Club lokacin da yake mataimakin shugaban kasa kuma shugaban kwamitin inganta tattalin arzikin kasa a wancan lokaci.

Daga nan ya bukaci Atiku, da ya yi taka tsan-tsan da ‘yan bani na iya, ya kuma hada kai da matasa da mata domin cimma nasara.

Da yake magana, Atiku ya bayyana jin dadin sa da ziyarar tare da jaddada kudirin sa na cigaba da tallafawa matasa da mata.

Ya kuma kara da cewa, a cikin kudirin sa neman zabe, ya fada cewa, mukamai a gwamnatin sa zasu kunshi kaso 70% na matasa, sannan zai ware dala biliyan 10 domin tallafawa matasan da kuma kanana da matsakaitan masana’antu a fadin kasar nan.

A cewar Atiku, domin samun dorewar demukradiyya a Najeriya, dole ne sai ‘yan kasa sun tashi haikan wajen korar jam’iyyar APC daga mulki, yana mai karawa da cewa babu wata hanya da zata tabbatar da wannan muradi face a samu hadin kan jam’iyyun adawar kasar nan.

Ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun AbdulRasheed Shehu, babban mataimakin sa akan abubuwan da suka shafi yada labarai, Atiku ya kara da cewa duk wani ‘dan jam’iyyar PDP dake adawa da wannan tsarin, magoyin baya ne na yunkurin da APC ke yi na maida kasar nan tsarin jam’iyya jam’iyya guda.