On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Yadda Kasuwar Hada-hadar 'Yan Wasa Ke Cigaba Da Gudana

Wasu daga cikin manyan rahotanni a kasuwar hada-hadar 'yan wasa

Real Madrid Ta Tabbatar Da Daukar Dan Wasa Antonio Rudiger

 

Awoniyi Zai Yi Watsi Da Tayin Forest

Dan wasan Najeriya, Taiwo Awoniyi na dap da yin fatali da tayin kungiyar kwallon kafa ta Nottingham, kungiyar da samu haurowa gasar Primayar Kasar Ingila a karshen kakar wasa da gabata.

Awoniyi, dan asalin Najeriya yace yana sane da cewa akwai wasu kungiyoyi da dama dake da sha'awar shiga zawarcin sa, a don haka ba zai yi hanzarin yanke hukunci akan makomar sa ba.

Liverpool Na Iya Bada Keita, a Yunkurin Ta Na Kawo Barella

Liverpool tace a shirye take ta mika Dan wasa Naby Keita a kokarin da take yi wajen ganin cewa ta sayi dan wasa Nico Barella daga Inter Milan.

Kungiyar na da burin mallakar wani dan wasa daga kasar Italiya, sai dai tana fatan musaya zata kasance cikin yarjejeniyar yin hakan.

Man U Zata Sake Sabon Lale Akan De Jong

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United tace zata sake mika sabon tayi da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona akan wasa Frankie De Jong.

Rahotanni sun bayyana cewa tayin farko da kungiyar ta yi bai yi kusa da abinda Barcelona ta nema akan dan wasan ba.

Sai dai yanzu Manchester United ta ce a shirya take ta kara yin wani sabon yunkuri domin samun nasara a wannan ciniki.

An Cimma Yarjejeniya Tsakanin Gotze da Eintracht Frankfurt

Dan wasa Mario Gotze na dap da komawa kungiyar kwallon kafa Eintracht Frankfurt.

Mujallar Sports1 ta rawaito cewa dan wasan, dan asalin kasar Jamus ka iya samun canjin sheka kowanne lokaci daga yanzu, bayan da ya shafe kakar wasanni biyu yana taka leda a wajen kasar sa.

Farashin Dan Wasa Diaby Ya Kai Euro Miliyan 50

An shar'antawa kungiyar kwallon kafa ta Newcastle biyan Euro Miliyan 50 a kokarin da take yi na sayen dan wasa Moussa Diaby daga Kungiyar Bayern Leverkusen.

Newcastle, mai buga gasar Primiyar kasar Ingila na wannan ciniki ne, a daidai lokacinda ita ma kungiyar PSG ke zawarcin dan wasan, sai dai ga alamu ciniki za ayi mai tsadar gaske.

Chelsea Za Ta Bude Tattaunawa Da Man City Akan Ake

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea na duba yiwuwar daukar dan wasa Nathan Ake daga Manchester City.

A dai dai wannan lokaci da kungiyar na ta kokari wajen kammala cinikin dan wasan gaba na City, Raheem Sterling, kuma tace akwai yiwuwar ta siyo duka yan wasan biyu.

Bayern Ta Sanyawa Barcelona Farashin Euro Miliyan 50 Akan Lewandowski

Bayern Munich na burin karbar Euro Miliyan 50 (£43m/$53m) a hannun Barcelona a cinikin da ake kokarin kullawa tsakanin kungiyoyin biyu.

Barcelona na ta kokari wajen ganin cewa ta mallaki dan wasan, sai dai Bayern ta yi watsi da tayin da kungiyar ta yi mata na karshe.

Sai dai duk da haka, rahotanni sun bayyana cewa Barcelona ta sake sabon lale domin mika sabon tayi akan dan wasan, wanda ake hasashen zai kasance tsakanin £40m tare da bonas da ka iya biyo baya.

Galtier Zai Karbi Ragamar Horas da PSG

Christophe Galtier, ya shirya tsaf domin karbar ragamar jagorancin kungiyar kwallon kafa ta PSG.

Shahararren dan jarida, Fabrice Hawkins ya rawaito cewa kungiyar ta birnin Farisa zata biya Nice Euro 10m wajen daukar mai horaswan.

 

More from Labarai