On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Yan Bindiga Sun Harbe Wani Lauya Har Lahira A Jihar Zamfara

MARIGAYI BARRISTER AZZA

Yan bindiga akan Babura sun harbe Wani lauya mai suna Benedict Azza har lahira a birnin Gusau na jihar Zamfara a ranar Alhamis, duk da dokar hana amfani da Babura da aka saka a jihar

An bindige lauyan ne lokacin da yake kan hanyar komawa gida da karfe 8 na dare kamar  yadda  shugaban kungiyar lauyoyi ta jihar Junaid Abubakar ya tabbatar ta cikin wata sanarwa da aka aikewa maname Labarai.

Sanarwar  ta baiyana cewa a ranar juma’a shugaban kungiyar ya samu kiran waya har ukku daga abokan aikinsa wadanda suke baiyana masa  harbe lauyan da aka yi, inda suka bar gawarsa a gefen titi dake kusa da ofishin hukumar kare afkuwar haddura na kasa reshen jihar dake birnin Gusau.

Kakakin rundunar yansandan jihar Zamfara  Mohammed Shehu ya tabbatar da  faruwar lamarin, Sannan kuma yace tuni aka baza jami’an yansanda domin zakulo wadanda suke da hannu cikin lamarin.