On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Coci A Jihar Katsina, Sunyi Garkuwa Da Mutane Sama Da 25

Wasu ‘yan ta’adda dauke da manyan bindigogi sun kai hari a majami’ar New Life dake karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, inda suka yi garkuwa da akalla mutane 25.

A cewar shaidun gani da ido, ‘yan ta’addan da ke kan babura sun mamaye cocin da ke unguwar Dan-Tsauni Gidan Haruna a safiyar Lahadi a lokacin da masu bauta  ke cikin cocin.

Babban mataimaki na musamman ga Gwamna Aminu Masari kan harkokin mabiya Addinin Kirista, Ishaya Jurau ya tabbatarwa manema labarai.

Yace a halin yanzu jami’an tsaro sun bazama kuma suna bakin kokarinsu wajen ganin an ceto duk wadanda al’amarin ya rutsa da su.