On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

'Yan Bindiga Sun Kone Offishin 'Yan Sanda A Jihar Anambra

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kona ofishin ‘yan sanda da ke garin Umuchu a karamar hukumar Aguata a jihar Anambra.

Wasu majiyoyi sun ce ‘yan bindigar sun kai farmaki ne da karfe 3 na dare  inda suka bankawa ginin ofishin  wuta.

Bayanai sunce ‘ya’yan kungiyar inganta garin  Umuchu, su ne suka gyara offishin a kwanakin baya, bayan da masu zanga-zanga suka lalata a yayin zanga-zangar EndSARS a shekarar 2020.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba’a samu labarin asarar rai ba sakamakon harin.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Tochu kwuIkenga, ya bukaci al’ummar yankin da su taimakawa ‘yan sanda da bayanai kan binciken da suke yi domin ganin an samu wadanda suka aikata laifin kone-kone da kuma gurfanar da su a gaban kotu.

More from Labarai