On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

'Yan Bindiga Sun Sace Wani Hakimi

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Hakimin Panyam a karamar Hukumar Mangu dake jihar Filato Adamu Derwan, Hakimin Panyam a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato.

Maharan sun farwa garin ne da sanyin safiyar Litinin kamar yadda  Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar filato, Alfredo Alabo ya baiyyana.

Ya kara da cewa  ‘yan bindigar sun kai  hari gidan Basaraken gargajiyar  sannan suka yi awon gaba dashi zuwa wani da har yanzu ba’a sani ba

Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar da umarnin daukar matakin gaggawa wajen zakulo wadanda suka yi garkuwa da basaraken, yayin da ake kira ga  al’umma dasu temaka da bayar da bayanan da zasu taimaka wajen kamo wadanda suka aikata laifin.

Satar Hakimin Panyam dai shi ne karo na biyar da ake garkuwa da sarakunan  gargajiya a jihar cikin watanni shida da suka gabata.

 

More from Labarai